Mutum 4 Sun Mutu, Yayin Da Mota Ta Afka Kan Masu Taron Biki A Belgium

Wata mota ta abka kan taron jama’a kasar Belgium yayin da suke tsaka da gudanar da wani taron biki, a safiyar ranar Lahadin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu 20, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

Magajin garin Jacques Gobert ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Belga cewa, “Mota da ke tafiya da gudun wuce kima ta shiga cikin jama’ar da suka taru domin halartar wani biki.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na safe (0400 agogon GMT) a wajen bikin Strepy-Bracquegnies, na gundumar tsohon garin La Louvriere, in ji hukumomi.

“A safiyar Lahadin nan, wata mota ta yi karo da… gungun mutane kusan 100 da suka bar dakin wasanni don komawa tsakiyar kauyen,” in ji ofishin magajin garin a cikin wata sanarwa.

“Hukumomi za su gudanar da taron manema labarai da karfe 11:00 na safe a La Louvriere domin bada cikakken rahoton kan lamarin” inji Magajin garin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram