Ni Fa Ban Ce A Mutu Ko A Yi Rai Sai Na Zama Gwamna Ba Na Dai Ce In Ni Ne Alheri Allah Ya Tabbatar – Inuwa

Sakataren gwamnatin jahar Katsina kuma mai son tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa ya ce, shi ba wai yana son zama gwamna ba ne ta kowane hali illa dai yana addu’a in shine alheri ga mutanen Katsina to Allah ya ba shi.

Mustapha Inuwa ya bayyana haka ne a yayin da ya shirya wani taro da ƙungiyoyi 286 da suke goyon bayan tafiyar shi a faɗin jahar.

KARANTA KUMA: Ban Yi Ma PDP Adalci Ba Da Na Yi Waƙar Shegiyar Uwa – Haruna Aliyu Ningi

Inuwa ya ce shi yana neman kuje rarar gwamna ne da zuciya ɗaya da kuma manufar samar da kyakykyawan shugabanci.

A cikin jawabin nasa da yi a gaban magoya bayan na sa ya kuma ce yana rokon Allah idan har ya bashi mulkin katsina to ya ba shi ikon yin abin da ya da ce in kuma ba zai ba shi damar yin abin kirki ba to kar Allah ya ba shi in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram