Rasha Ta Kai Hari Na Biyu Da Makami Mai Linzami, Ya Lalata Rumbun Aje Man Fetur Na Ukraine – Ma’aikatar Tsaro

Ma’aikatar tsaron Moscow ta sanar da cewa, dakarun kasar Rasha sun kai wani hari na biyu da makami mai linzami na Kinzhal da kan wani yanki na kasar Ukraine.

Hukumomin kasar sun ce harin da aka yi amfani da sabon makami mai linzami na Kinzhal na kasar Rasha ya lalata wani wurin ajiyar man fetur a kudancin kasar.

“Kinzhal…makami Mai linzami Wanda ake kiyasta cewa ya nunka gudun sauti sau goma ya lalata wani katafaren wurin ajiyar man fetur na sojojin Ukraine kusa da matsugunan Kostyantynivka da ke yankin Mykolaiv,” in ji hukumomin kasar ta Rasha.

Kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito cewaz ba za ta iya tabbatar da wannan ikirari da kanta ba, ko da yake zai kasance rana ta biyu a jere da Rasha ta kai hari kan wuraren Ukraine da irin wanan makami idan har gaskiya ne.

Jami’an Rasha sun ce makamin Kinzhal na iya kaiwa wani wuri mai nisan kilomita 2,000 (mil 1,240) sannan ya tashi da sauri Kuma yayi tafiyar fiye da kilomita 6,000 (3,728mph).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram