Yakin Rasha Da Ukraine: Lokaci Ne Kawai Zai Tabbatar Da Ɓangaren Da Muke Goyan Baya — China

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, “lokacin ne zai tabbatar da cewa ga matsayin kasar Sin awasu lamura na tarihi” a daidai lokacin da ake ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

Wang Yi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin, yayin da yake zantawa da manema labarai, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.

“Kasar Sin za ta ci gaba da yanke hukunci na kashin kanta bisa cancantar lamarin da kuma bisa gaskiya da adalci.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ba za mu taba amincewa da duk wani tilastawa da matsin lamba daga wata kasar waje ba, kuma muna adawa da duk wani zargi da zato mara tushe balantana makama kan kasar Sin.”

Wang ya ce, “Maganin dogon lokaci shi ne a yi watsi da tunanin yakin cacar-baki, da kaucewa shiga cikin fadace-fadacen kungiya, da samar da daidaito, inganci da dorewar tsare-tsaren tsaro na yankin. Ta haka ne kawai za a iya samun kwanciyar hankali na dogon lokaci a nahiyar Turai.”

Idan za’a iya tuna cewa yaki tsakanin Ukraine da Rasha ya fara ne a watan Fabrairun da ya gabata.

Yakin ya shiga kwana na ashirin da uku a kemn a yau lahadi, inda tuni aka samu hasarar dimbin rayuka da kadarorin milliyoyo.

Tun da fari Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ne ya ba da umarnin mamaye kasar Ukraine bisa rashin jituwa kan wasu batutuwan siyasa a tsakanin bangarorin biyu.

Putin ya kuma lissafo wasu sharuddan domin a cikamasa kafin kawo karshen yakin da yake kan yi da kasar ta Ukraine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram