Abun Magana Ya Samu: An Sace Motar Ɗan Jarida A Sakariyar Jam’iyar APCn jihar Kaduna

An sace wata mota kirar Golf 3 samfurin Amurka mai lamba LSD-516-HB mallakin Editan fannin siyasa a Jaridar New Nigerian Newspaper (NNN), Amos Mathew.

An yi fakin din Motar ne a gaban sakatariyar jam’iyyar APC mai launin baka, inda aka gayyaci ‘yan jarida domin gabatar da rahotannin bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar APC.

Mista Mathew ya ce, ya ajiye motar ce a gaban Sakatariyar jam’iyyar da misalin karfe 10:00 na safe, kuma an gano ta bace ne a karshen taron siyasa da wasu ‘yan bangar siyasa da ba a san ko su waye ba suka sace ta da misalin karfe 11:20 na safiyar ranar Talata.

“An sanar da ‘yan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa game da sace motar,” in ji shi.

“Sauran kayayyaki masu daraja a cikin motar sun hada da katin ATM, katin shaida na aikinsa, katin zabe, katin shaidar zama dan kasa da dai sauransu,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram