An Tsinci Gawar Wata Mata A Ɗakin Otal A Benue

Wata mata, wacce har yanzu ba a bayyana sunan ta ba, an tsinci gawar ta a karshen mako a cikin wani otal da ke Nyiman layout cikin babban birnin Makurdi a jihar Benue.

Rundunar ‘yan sandan ta shaida wa wakilinmu a Makurdi a ranar Litinin da ta gabata cewa, an kama wasu mutane uku da ke da hannu a cikin lamarin.

A baya wakilinmu ya tattaro daga majiya mai tushe cewa matar ta kasance cikin masu damfarar yanar gizo da aka fi sani da Yahoo boys, inda ta kara da cewa an cire mata sassan jikin ta.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ta kara da cewa maganar zargin da ake yi na bacewar wani sassan jikin ta ba gaskiya bane, inda ta ce an gano gawar ba tare da wata alama ba a jikin ta.

Anene ta ce, “Akwai rahoton mutuwar wata mace a cikin otal, amma cikakkun bayanai za su fito ne daga likitoci.

Kodayake ba mu ga alamun tashin hankali ba don haka binciken gawar zai bayyana musabbabin mutuwar ta ta.

Kazalika tace “An kama mutane uku da ake zargi da hannu a cikin lamarin, don haka za su ba mu cikakken bayani. Ba za mu iya cewa lamarin kisan kai ba ne tukuna.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram