Abun Murna: Cikin Sati Ɗaya, Ƴan ISWAP 7,000 Sun miƙa Wuya — Inji Soji

Mayaƙan ISWAP 7,000 ne su ka miƙa wuya ga rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya a mako ɗaya da ya gabata.

Kwamandan Rundunar ‘Operation Hadin Kai’, a Arewa-maso-Gabas, Christopher Musa ne ya baiyana haka ga Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Laraba a Maiduguri.

Musa ya tabbatar da cewa a na samun nasara sosai a yaƙin da sojoji ke yi da ƴan ƙungiyar ISWAP da Boko Haram.

“Wannan a bayyane ya ke duba da dubban ‘yan ta’addan da suka hada da mayaka, wadanda ba mayaka ba, ƴan barandansu tare da iyalansu ke ci gaba da ajiye makamansu a sassa daban-daban na Borno domin karbar zaman lafiya,”

Musa ya ƙara da cewa sojoji za su ɗauki bayanan yan ta’addan da iyalansu da su ka miƙa wuya kafin a fara yi musu shirin gyaran hali.

Kakakin ya ƙara da cewa rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da zabe rantse wajen kawo karshen Boko Haram da gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram