Babbar Nasara ce Ga Al’ummar Jahar Cross Rivers da Kotu Ta Kori Ƴan Majalisu 20

Jam’iyyar PDP a Jahar Cross River ta bayyana cewar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya tayi dake Abuja, tana korar Ƴan Majalisu 20 da suka koma Jam’iyyar APC daga PDP, “wata nasara ce ga ƴan Jahar Cross River.”

Hukuncin dai Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya yanke shi a cikin wata ƙara da aka shigar masa mai lamba FHC/ABJ/CS/975/2021 wanda Jam’iyyar PDP tayi.

A cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa na Jam’iyyar Mike Ojisi Jam’iyyar ta taya ƴan Jahar murnar tsayawa tsayin daka da PDP, tana mai basu tabbacin nasara anan gaba.

“Shugaban Jam’iyyar PDP na Jahar Barr Venatius Ikem yayi kira mambobin jami’iyyar dasu yi amfani da canja sheƙa da ake yi a wata. Afrilu” su dawo Jam’iyyar.

Shugaban Jam’iyyar ya bayyana fatan cewa Hukuncin za’a zartar dashi yadda ta kamata ga waɗanda lamarin ya shafa.

“Jam’iyyar PDP tayi kira ga ƴan Jam’iyyar dasu zama masu jajircewa a kowa ne lokaci ga Jam’iyyar domin amso masu nasarar su da APC ta sace.”

A jawabinshi, Sakataren Yaɗa Labaru na Jam’iyyar APC a Jahar Cross River Mr Erasmus Ekpang, yace Jam’iyyar nada kwanaki 90 domin jin abinda zai fito daga Ɗaukaka ƙarar a da suka yi.

“Ko hukuncin ai baice a canja ƴan Majalisar da wasu na PDP ba, abinda ka iya faruwa shine ana iya cewa ayi sabon zaɓe a Kotun Ɗaukaka ƙara data Ƙarshe.

“Jam’iyyar APC ta ɗauki hukuncin da kyakkyawar manufa, kuma tana da kwarin gwiwa ga Kotu, kuma tana fata idan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta maido masu da nasarar su, PDP zata ɗauki
hukuncin da Kyakkyawar manufa, kamar yanda muka yi,” Inji shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram