Dara Taci Gida: Lauya Ya Maka Ƙungiyar su Ta Lauyoyi A Kotu, Ya Nemi A Miliyan 10 Na Ɓata Suna

Wani Lauya Bartholomew Okafor-Oyilo, ya buƙaci Babban Kotu a Abuja data ajiye abinda Ƙungiyar Lauyoyi ta bayyana akan shi, wanda ya buƙaci a yi mashi hukunci akan ra’ayin shi daya bayyana na Shari’a a matsayin sa na Babban Mai Taimakawa Mataimakin Gwamnan Jahar Anambra akan ɓangaren Shari’a.

Mai Shigar da Ƙarar a jawabin shi daya gabatar akan Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa NBA da Sakataren Kwamitin Hukunci na NBA, yace shi bai yanke hukunci bane kamar yadda aka binciko a kanshi.

Okafor-Oyilo a rubutun da yayi, wanda ƴan Jarida suka samu a ranar Talata, yace ya rubuta ra’ayin sa ne ga Mataimakin Gwamnan Jahar Anambra na Lokacin, wanda kuma shine Shugaban Kwamitin Sasanci akan Ƙasa a Al’ummomin Ukpo da Abba a Jahar Anambra.

A cewar sa, wannan ra’ayin wasu suka fitar dashi akan wannan rikicin Kasa.

Yace ” a ranar 24 ga watan yunin Shekarar 2019, masu neman yadda za’a tsara iyaka akan rikicin Kasar dake faruwa, suka rubuto man takarda ta hanyar Lauyoyin su, suna buƙatar in bada shawara ta akan wannan lamari.

Okafor-Oyilo yace NBA ta rubuto mashi takardar neman bayanai, kuma ya maida masu da jawabai akan haka.

Lauyan yace mai samu wata gayya ta daga Ƙungiyar ba domin ya saurari abinda ake tuhumar sa ba, kawai sai dai ya karanta a Jarida cewa an gayya ce shi zai fuskanci Kwamitin Ladaftarwa.

Daga sai ya buƙaci Kotu ta bayyana wannan bincike da aka yi akan shi a matsayin wanda bai halatta ba, bai cika ƙa’idoji ba.

A lokacin da yake kira ga Kotu data jefar da binciken da Shawarwarin ya buƙaci Kotu data bashi tarar Naira Miliyan 10 akan Ƙarar da aka shigar akan shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram