NBTE Ta Amince wa Kwalejin Harkokin Mulki Ta Bala Abdullahi Funtua Karantar Da Wasu Sabbin Kwasa-kwasai

 

NBTE ta Amince wa Kwalejin Harkokin Mulki ta Bala Abdullahi Funtua Karantar da wasu Sabbin Kwasa-kwasai

Kwalejin Harkokin Mulki ta Bala Abdullahi dake Funtua, na sanar da Al’umma cewa, Hukumar Kula da Ilmin Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na Ƙasa (NBTE) ta amince mata , ta fara karantar da wasu sabbin Kwasa-kwasai, a zangon Karatun wannan Shekarar ta 2021/2022.

Sabbin Kwasa-kwasan da Hukumar NBTE ta amincewa Kwalejin Sun Ƙunshi ND Computer Science, da ND Office Technology and Management (OTM) da Kuma ND Public Administration.

A cewar ta, dukkanin Ɗalibin dake da Sha’awar yin Karatu a Kwalejin, kuma ya samu nasarar cin maki 100 a Jarabawar JAMB da sama da haka a Jarabawar UTME ta 2021, ana kiran shi daya ziyarci cibiyar da aka amince ayi Jarabawar JAMB mafi kusa dashi, domin ya zaɓi Kwalejin a matsayin ta farko.

Haka zalika, duk Ɗalibin dake da Sha’awar shiga Kwalejin zai kasance yaci Darussa 5 ko sama da haka tare da cin Darasin Turanci da Lissafi.

Hakanan kuma Ɗalibi zai ɗora Jarabawar Kammala Sakandiren shi a shafin rajistar Ɗalibai na JAMB.

Ɗaliban da suka samu nasara ana saran zasu karɓi Admission na Karatun tare da fito da Takardar Shaidar Gurbin Karatu da aka bashi, wadda da’ita ce zai gabatar wa Kwalejin a lokacin shirin tantance su.

Domin Ƙarin Bayani, ana iya tuntuɓar Jami’in dake Kula da Bada Guraben Karatu na Kwalejin Usman Shehu, ko kuma a kira Lambar sa 08034205849

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram