An Kama Wani Manomi Bisa Zargin Kashe Mahaifiyar Sa Da Dan Uwan Sa A Jahar Kwara

An Kama Wani Manomi Bisa Zargin Kashe Mahaifiyar Sa Da Dan Uwan Sa A Jihara Kwara

Wata Kotun Majistare da ke Ilorin ta bayar da umarnin tsare wani manomi, Mufutau Adekola, a gidan yari na Oke-Kura bisa zargin kashe mahaifiyarsa da dan uwansa.

Rundunar ‘yan sandan ta tuhumi Adekola da laifin kisa wanda ya sabawa tanadin sashe na 221 na dokar manyan laifuka.

Lauyan masu shigar da kara, Insp Folorunsho Zacheaus, ya shaida wa kotun cewa Adekola ya kai wa mahaifiyarsa, Rafatu da kuma yayansa, Mukaila hari, a lokacin da suke barci a ranar 9 ga Watan Maris, a Oke-Ode a karamar hukumar Ifelodun ta jihar.

Alkalin kotun, Ibrahim Dasuki, wanda bai dauki karar Adekola ba saboda da rashin hurumi, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi, har sai an kammala bincike.

Dasuki ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 25 ga watan Afrilu domin ci gaba da bayyana lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram