APC Ta Haramtawa Masu Rike Da Mukaman Siyasa Kada Kuri’a A Babban Taron Ta Na Kasa

Jam’iyyar APC ta haramtawa masu rike da mukaman siyasa kada kuri’a a babban taronta na kasa da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

Wannan dai ya yi dai-dai da tanadin sashe na 84(12) na dokar zabe ta 2022 wadda ta haramta wa masu rike da mukaman siyasa kada kuri’a ko yin zabe a yayin babban taro ko zabe.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar Alhamis mai taken, “Hankali ga masu rike da mukaman siyasa da aka zaba a matsayin wakilai”, jam’iyyar ta ce, “Kwamitin tsare-tsare na musamman na riko na jam’iyyar APC ya bayyana cewa duk wadanda aka nada a siyasance da aka zaba a matsayin wakilai a Babban taron kasa da aka tsara a ranar 26/3/2022 BA ZAI Yi ZABE BA duba da cece-kucen da ke tattare da sashe na 84 (12) na dokar zabe, 2022.

“Duk da haka, masu nadin mukaman siyasa na iya halarta a matsayin masu sanya ido.”

Wannan wani ruguje ne na sashe na 84(12) na dokar zabe mai cike da cece-kuce da ya hana duk wanda aka nada za a zaba ko kuma zama wakilai a yayin babban taron.

Sai dai Majalisar ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram