Da Ɗumi-Ɗuminsa: Kotu Ta Dage Yanke Hukunci Kan Sauya Shekar Gwamna Ayade

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Afrilu kan karar da ke neman tsige gwamnan Kuros Riba, Ben Ayande da mataimakinsa, Ivana Esu kan ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Mai shari’a Taiwo Taiwo ya shirya yanke hukuncin ne a ranar 25 ga watan Maris, 2022.

Amma, lokacin da jaridar The Nation ta ziyarci kotun a safiyar yau, an nuna ta a cikin jerin dalilan cewa za a yanke hukuncin a ranar 6 ga watan Afrilu.

Karar mai lamba: FHC/ABI/CS/975/2021 PDP ce ta shigar da ita, inda INEC, Ayade, Esu da APC a matsayin wadanda ake kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram