An Kama Ɗan Sandan Daya Tursasawa Direba Neman Ya Bashi Takardar Shaidar Iznin Sanya Baƙin Gilashi

An kama wani sifeton ‘yan sanda, Dele Reuben, bisa zargin tursasa wani direba a Legas kan bukatar nuna takardar izinin Saka bakin gilashin mota wato Tinted.

Kamen nasa ci gaba ne ga wani faifan bidiyo na dan sandan Lokacin da ya ke neman wani direban mota ya ba shi kudi saboda rashin takardar izinin Saka bakin gilashin motarsa.

Idan dai za a iya tunawa, Sifeto Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba, ya gargadi ‘yan sanda da su daina neman lasisin Saka bakin gilashin Mota daga wajen direbobi.

A halin yanzu dai ana tuhumar Insfekta Reuben a sashin provost na hedikwatar rundunar dake Ikeja.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abiodun Alabi ne ya bayar da umarnin kama jami’in.

Hundeyin ya ce an dauki sufeto Dele Reuben a wani faifan bidiyo yana tursasa wani direba don neman izinin da aka dakatar da shi, Dan Sanda ya nema a yanzu.

Ya ci gaba da cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya nanata wa jami’ansa kan illar dake tattare da rashin hakuri da cin zarafin al’uma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram