An Kama Masu Yankan Aljihu A Wurin Babban Taron APC Na Ƙasa

An cafke wasu mutum uku da ake zargi da yankan aljihu jama’a a wajen babban taron jam’iyar APC da ke gudana a Abuja, bayan kama su suna satar wayar salula a kofar shiga filin taron.

BBC ta ce, wani jami’in tsaro ya faɗa wa kamfanin labara na Najeriya NAN cewa waɗanda aka Kama ɗin sun faki idon dandazon al’ummar da ke kofar shiga filin taron na Eagle Square wajen sace wayoyinsu.

Jami’in tsaron ya ƴara da cewa waɗanda ake zargi da sace wayoyin sun haɗa baki wajen aiki tare, inda suke sace wayoyi da kuma kuɗin mutane da ke filin taron.
Har wa yau, jami’in tsaron ya ce an samu damar kama mutanen ne da taimakon sauran abokan aikinsu ‘yan sanda da ke sanya ido a kofar shiga Eagle Square yayin da wakilai ke shiga domin kaɗa kuri’arsu.

Ya ce za a kai waɗanda ake zargin zuwa shelikwatar ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram