Hukumar kula da al’umma a Afghanistan na gudanar da bincike a gaban ofisoshin gwamnatidomin duba ko tsawon gemun ma’aikata ya kai wanda hukuma ta umarta, da kuma lura da sanya kayayyaki kamar yadda Musulunci ya buƙata.
KARANTA KUMA:Yellow: Ɗan Takife Mai Yi Ma Kamfanonin Sadarwa Sata.
Ma’aikatar yaɗa Kyawawan Halaye da Hana Aikata Laifuka ta gargaɗi ma’aikatan gwamnati cewa za su iya rasa ayyukansu idan ba su mayar da hankali kan waɗannan dokokin ba.
BBC ta ruwaito cewa, batun na cikin sabbin dokokin da ƴan Taliban suka kafa a makonnin nan.
An kulle makarantun sakandare na mata cikin sa’o’i bayan da daliban suka koma hutu a makon jiya.