Rahotanni dake fitowa daga Jihar Niger a tarayyar Najeriya sun nuna cewa Yan ta’adda sun Kwashe Kwanaki biyu suna addabar kauyukan Chibani da kuma Gini dake a yankin karamar hukumar Munya.
Kakaki Net Work ta ce, ko a ranar Litinin ɗin nan kafar sadarwa ta Niger State Media News 24 ta wallafa a shafinta ance an hango yan ta’adda suna shawagi a yankin cikin walwala.