Ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi, ya roki ‘yan Najeriya da su taimaka da kudade domin yi wa wadanda harin jirgin kasa ya rutsa da ranar Litinin.
Kimanin mutane 9 ne suka rasa rayukan su a yayin da wasu da dama suka samu raunuka a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan da ke kan hanyar sa ta zuwa Kaduna daga Abuja hari.
KARANTA KUMA:Kwastan Sun Kama Buhunan Aya Da Na Shinkafa A Katsina
Amaechi, wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya afku a ranar Talata, ya ce, harin, da an dakile idan da ba a samu cikas ba wajen sayo manyan na’urorin daukar hoto da masu sunsuna na nera biliyan 3 da akai niyyar kakkafawa a kan hanyoyin jirgin kasan.
Ya ce idan har aka samu wadannan na’urori babu shakka za a kawar da duk wani tarnakin da ke hana ganin wasu boyayyun abubuwa a kan hanyoyin jiragen kasa a fadin Najeriya.
Da ya ke magana a sa’ilin da ya ziyarci wadanda harin ya rutsa da su kuma su ke karbar magani a asibitin sojin kasa da ke Kaduna a ranar Laraba, ministan ya ce sojojin sun yi wa mutanen magani ne ba tare da amsar ko kwabo ba daga hannunsu.
Duk da haka, ya ce wasu daga cikin marasa lafiyar na bukatar wasu magunguna da ba a yin su a kasar, inda ya bukaci ‘yan Najeriyar da su taimaka da aljihunsu wajen domin a samu sayo magungunan.
A cewar Amaechi, wasu mutanen sun samu kuna mai tsanani sannan wata mata na da harsashi a cikin zuciyar ta kuma hukumomin asibitin za su kawo kwararru domin duba yadda za a yi mata aiki.
Ya ce, shi da ma’aikatar sa a madadin gwamnatin tarayya, na jinjina wa hukumomin sojin kasan Najeriya bisa karamcin.