Dubban Magoya Baya Sun Ce Katsina Ta Dikko Radda Ce

Shugaban hukumar kula da ƙanana da matsakaitan sana’o’i na Najeriya Dr, Umar Dikko Radda ya bayar da tallafin kayayyaki na milyoyin naira ga shuwagabannin mazaɓu na jam’iyyar APC na ƙananan hukumomin Ɓatagarawa da Rimi da Charanchi na jahar Katsina.

Taron bayar da tallafin ya gudana ne a ranar Assabar ɗinnan a ƙaramar hukumar Rami inda dubban magoya bayansa haɗe da ƴan takarkari a matakai daban-daban suka halarci taron tare da nuna cikakken goyon bayansu gare dangane da gurinshi na zama gwamnan jahar ta Katsina.

Dikko Radda a wajen taron ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar ta APC da ma masu goya ma ƴan takarkari baya da su kasance masu haƙuri da kuma haɗa kansu domin samun nasarar jam’iyyar.

Karanta wannan labarin:Kada Ku Kuskura Ku Take Haƙƙin Ƴan Jarida, Ƴan Najeriya – IG Ya Gargaɗi Ƴan Sanda

Hakazalika ya faɗi abubuwa da ya rarraba a wurin da suka haɗa da motoci 3 da babura 10 da buhunan shinkafa da gero da masara tare da dubu 10 ga wasu mutane 368 da dai sauransu.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan ƴaƴan jam’oyyar APC da kwamishinan ilimi na jaha da masu neman kujerun siyasa a yanki a matakai daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram