Muttaqha Rabe Darma na ɗaya daga cikin mutanen da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar gwamna a jahar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
To sai dai Muttaqha Darma ya bayyana damuwarshi game da yadda fom ɗin takarar gwamnan ya yi tsada inda jam’iyyar ta sanya ma shi kuɗi har kimanin milyan 21.
Ya bayyana haka ne a yayin da ya shirya wani taro dangane da wasu littattafai da ya rubuta waɗanda a ciki ya kawo wasu mihimman hanoyi da shugabanni zasu bi su kawo ma jahar ci gaba mai ɗorewa.
Ya ce wannan ba komai ba ne illa koya ma yan siyasa yadda za su saci kuɗin al’umma idan suka hau kan karagar mulki in aka yi la’akari da yadda suka sayi fom ɗin da tsada.
Darma ya ce lamarin na son ya koma kamar wasu ƙungiyoyin asiri dole sai kai wane ne ko kuma ɗan wane ko ƙanen matar wane sannan a ke yi da kai.
Ya na mai kira ga al’umma da maida hankali game da lamarin su fito su nuna rashin amincewarsu domin acewarshi su ne ake ƙwara tunda su ake satar ma kuɗaɗe.