Kada Ku Kuskura Ku Take Haƙƙin Ƴan Jarida, Ƴan Najeriya – IG Ya Gargaɗi Ƴan Sanda

Sufeto-Janar na Ƴan Sandan Najeriya Usman Baba ya bayyana cewar Rundunar ko kaɗan bazata amince da cin zarafin ƴan Jarida ba da sauran Ƴan Najeriya.

A wani taro da Cibiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa da Ƙasa ta Najeriya, Baba yace ƴan sanda suna mutunta irin gudunmawar da ƴan Jarida suke bayarwa, kuma zasu haɗa hannu da Kafafen Yaɗa Labaru domin inganta tsaro, da kare haƙƙi da Adalci.

Baba ya jaddada cewa Hukumar da Kafafen Yaɗa Labaru ƴan uwan juna ne, dukkanin su suna aiki ne saboda abu guda ɗaya, duk da sun bambanta.

“A saboda haka yana matuƙar amfani ga Ƴan Sanda, a yayinda Kafafen Yaɗa Labaru suka je suna aikin su, zata iya yinshi ba tare da tsoro ba da kuma tsaro .

Shugaban Ƴan Sandan yasha alwashin ɗaukar mataki akan Jami’an Ƴan sanda da suka karya haƙƙoƙin ƴan ƙasa, musamman Ƴan Jarida.

“Kofar mu a buɗe take, kuna iya kawo irin waɗannan karya dokoki a garemu”, ya bayyana yana mai roƙo da aka cigaba da wayar wa Al’umma kai akan aikace-aikacen Ƴan Sanda.

“Muna Son Al’umma su fahimta tare da mutunta iyakokin su, musamman a lokacin zanga-zanga da wani ibtila’i”.

Shugaban Hukumar Kula da Ƴan Jarida na Ƙasa Musikilu Mojeed yayi ƙorafi akan yadda ake cin zarafin ƴan Jarida, wanda aka kama, akaci mutuncin su tare da ɗaure su.

Yace wannan lamari shiya janyo aka maida Ƙasar koma baya ta hanyar lissafa a ranar Ƴancin Ƴan Jarida ta ƙasa, inda ƙasar tazo ta 120 cikin 180.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram