Matsafi Ya Kashe Ƙananan Yara 9, Ya Binne su A Taraba

Wani da ake zargin mai suna Mubarak Lamu ya amsa laifin kashe yara maza 9 tare da binne su a kaburbura daban-daban a wani yanki na jihar Taraba.

A makon jiya ne ‘yan sanda suka kama Mubarak mai shekaru 30 a garin Mutumbiyu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba bisa bacewar wani yaro dan shekara shida.

Wanda ake zargin ya amsa laifin kashe yaron tare da binne shi a kogin Dan Kuturu a cikin garin Mutumbiyu.

Mazauna yankin sun ce wanda ake zargin ya jagoranci tawagar jami’an ‘yan sanda zuwa wurin inda aka tono gawar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wanda ake zargin ya kuma amsa laifin kashe wasu yara maza guda tara tare da binne su a wurare daban-daban domin gudanar da aihiri.

Furucin wanda ake zargin ya tayar da hankula a garin yayin da wasu fusatattun matasa ciki har da ‘yan uwan ​​yaran da ake zargin matsagin ya kashe su sun yi yunkurin kona gidan wanda ake zargin.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce yana jiran cikakken bayani kan lamarin daga hedikwatar ‘yan sanda ta Mutumbiyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram