Fitattacen malamin nan na addini wato Sheikh Nuru Khalid ya bayyana matsayarsa game da huɗubar juma’a da yayi a juma’ar da ta gabata wadda har ta yi silar dakatar da shi daga limancin a masallacin Apo da ke Abuja.
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wata fira da ya yi da yan jarida inda ya ce shi a shirye ya ke ya amshi duk abinda Allah ya hukunta akan sa game da maganar sha’anin tsaro a Najeriya.
Karanta wannan labarin:Za mu Ƙwace Mulkin Zamfara Daga Hannun Matawalle – Cewar Sanata Marafa
Haka kuma malamin ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da tafsiri a wannan wata na Ramadana.