Masari Ya Ce A tarihi Najeriya Ba Ta Taɓa Samun Shugaba Mai Son Ci Gabanta Ba Kamar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce, Najeriya ba ta taba samun shugaban da ke son ci gaban ta ba kamar Muhammadu Buhari.

Masari ya bayyana matsayin na sa ne a lokacin wani gangamin da masu amfana da shirin inganta rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya, NSIP, su ka shirya a jihar.

Karanta wannan labarin:A kan Maganar Tsaro A Najeriya A Shirye Na Ke Da Duk Abinda Zai Same Ni – Sheikh Nuru Khalid

Gwamnan wanda ya sha kokawa dangane da yadda matsalar rashin tsaro ke addabar jihar ta Katsina, ya ce, tun daga lokacin da Najeriya ta cure a shekarar 1914, ba ta taba samu shugaba kamar Buhari ba.

Masarin wanda ya yi furucin a ranar Asabar ya ce, shugaba Buhari ya aza wani kwakkwaran harsashen da idan har shugaba mai zuwa zai yi yakkyawan amfani da shi, zai taimaka wajen fitar ‘yan Najeriya da dama daga kangin talauci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram