Mu So Mu Ke Yi Malamai Su Rinƙa Yin Huɗubar Da Ta Ke Kwantar Da Hankalin Ƴan Najeriya Ba Su Tunzura Su Ba – Sanata Ɗansadau

Sanata Sa’idu Muhammad Ɗansadau ya bayyana irin kalamai da huɗibobin da ya kamata malamai su rinka yi a yayin tsokaci dangane da halin da Najeriya ta ke ciki game da rashin tsaro.

Sanatan wanda shi ne shugaban kwamitin masallacin rukunin gidajen ƴan majalisun tarayyar Najeriya da ke unguwar Apo a Abuja inda babban malamin nan da kwamitin ya dakatar, Sheikh Nuru Khalid ya ke limanci, ya faɗi hakan ne a yayin wata fira da yayi da wakilin BBC hausa ta wayar salula.

Sanata Ɗansadau ya ce halin da ƙasar nan ta ke ciki an harziƙa mutane kuma kowa zuciyar ta kawo a wuya don haka bai kamata ba malamai su rinka kalamai da zasu kara harzuƙa mutane.

Ya ce kafin su dakatar da malamin saida ya sha karɓar ƙorafe-ƙorafe game da malamin akan a yi ma shi magana ya daina abubuwa da ya yawan faɗa masu kama da tunzura yan Najeriya.

Sheikh Nuru Khalid dai ya yi huɓar juma’ar da ta gaba inda kuma ya yi maganganu game da matsalar tsaro har ma ya ke cewa in zaɓe ya zo ƴan Najeriya su ce ba za su yi zaɓe ba sai an yi maganin kashe-kashen bayin Allah sannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram