Za mu Ƙwace Mulkin Zamfara Daga Hannun Matawalle – Cewar Sanata Marafa

Tsohon dan majalisar tarayya da ya wakilci shiyyar Zamfara ta tsakiya tsakanin 2021 zuwa 2019, Sanata Garba Kabiru Marafa ya bayyana cewa babu wani ikon da zai sa Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya ci gaba da zama a kujerarsa bayan 2023.

Ya ce babu dalilin da zai sa Gwamna Matawalle ya ci gaba da lalata dukiyar Jihar Zamfara.

Sai dai bai bayyana ko kungiyarsa za ta fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa wata jam’iyyar ba.

“Yanzu mun shirya yin tawaye ga gwamnati mai ci a jihar ta hanyar gagarumin juyin juya hali saboda jama’a sun gaji da duk wadannan matsaloli a jihar,” in ji shi.

Jam’iyyar APC a Zamfara ta fuskanci rikici biyo bayan gudanar da babban taron jam’iyyar na jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram