Ƴan Bindiga Sun Harbe Ɗan Kwamishinan Tsaron Jahar Zamfara

An harbe dan DIG Ibrahim Mamman Tsafe ( Mai ritaya), kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Zamfara mai ci.

Jaridar Daily Trust ta fahimci cewa an kashe dan Tsafe tare da wasu mutane uku a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari garin Tsafe, hedikwatar karamar hukumar Tsafe ta jihar a daren ranar Lahadi.

A baya-bayan nan dai, garin Tsafe da wasu al’ummomi da dama a cikin karamar hukumar sun sha fama da munanan hare-hare da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Watanni biyu da suka gabata an kashe wani mazaunin garin da jami’in kwastam a wasu hare-hare da aka kai a garin.

A watan Fabrairun da ya gabata ne ‘yan bindigar suka harbe wani limami a lokacin da yake kiran sallar subhi a garin Magazu da ke da tazarar kilomita 5 kudu da garin Tsafe.

Yan ta’addan da ake kyautata zaton suna tserewa ne daga ayyukan soji a wasu sassan jihohin a hankali suna mayar da sassan karamar hukumar Tsafe zuwa wasu sabbin mafakan su.

Mazauna garin sun shaida wa majiyar Jaridar Daily trust cewa ‘yan ta’addan sanye da kayan sojoji sun kai farmaki unguwar Shiyar Namada da ke kusa da gidan kwamishinan inda suka bude wuta kan mutane.

“Wasu mazauna garin da suka gan su tun da farko sun dauke su a matsayin jami’an tsaro da ke sintiri a yankin na yau da kullum

“Dan kwamishinan, tare da wasu mutane suna zaune a gaban gidan DIG Ibrahim Mamman Tsafe a lokacin buda baki, kwatsam sai ga ‘yan bindigar suka fito suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

“A yayin harin, galibin mutanen da ke sallar Tarawihi a masallatai da dama da ke kewayen yankin kuma mazauna yankin sun gudu zuwa domin Neman tsira da rayukan su. Daga baya ‘yan bindigar sun janye zuwa cikin dajin. Kamar yadda nake magana da ku, ina gidan Waziri ne inda ake shirye-shiryen jana’izar su,” in ji wani mazaunin unguwar mai suna Umar.

Wasu mazauna garin sun shaida wa wakilin Jaridar Daily Trust cewa, harin na iya zama ramuwar gayya, saboda wani da ake zargin dan fashi ne da aka gani a kofar garin a ranar Juma’ar da ta gabata, sai jami’an ‘yan banga da aka fi sani da ‘Yan Sakai suka fille kansa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ba a Sami Ji ta bakinsa ba har ya zuwa lokacin mika wannan rahoton.

Kazalika duk kokarin da Akayi domin samun amsar kwamishinan ma abun ya ci tura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram