Ƴan Najeriya Miliyan 2 Zasu Fara Karɓar Biliyan N20bn duk wata-wata Daga Watan Yuni – Sadiya Farouk

Gwamnatin tarayya tace zata fara raba wa yan Najeriya Naira Biliyan N20bn daga watan Yuni a tsarin tallafi karkashin shirin National Cash Transfer, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Bayanai sun nuna cewa gwamnatin tarayya zata biya yan Najeriya miliyan biyu N5,000 a shirin Basic Cash transfer da kuma ƙarin N5,000 a tsarin tallafawa talakawa.

Wanda yake jimullar kudin da Gwamnatin tarayyar zata kashe zasu kai biliyan N20bn kan mutanen da zasu amfana.

Wani bayani da ya fita a watan Maris, 2022 kan dabaru da kuma tsarin harkokin ma’aikatar jin ƙai da walwalar al’umma ya nuna cewa yan Najeriya dake amfana da shirin ƙara ƙaruwa suke.

Saboda haka ‘yan Najeriya ku shirya 2022 ne za ku sha jar miyar Baba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram