Ƴan PDP Da APC Na Kuka Game Da Tsarin Sansanci Da Jam’iyyun Ke Yi Wajen Tsayar Da Ƴan Takara – A Taraba

Al’ummar jihar Taraba sun koka dangane da tsarin sasanci wajen fitar da ‘yan takara a karkashin jam’iyyu kamar dai yadda ake gani jihohi da dama, inda su ka ce wani sabon salo ne na cusa wa jama’a ‘yan takarar da ba su cancanta ba.

Kamar yadda suka bayyana a ranar Litinin, mazauna Taraban sun ce hakan wata barazana ce ga samun kyakkyawan shugabanci domin zai kara ta’azzara take-taken cin hanci da rashawa tare da kara jefa al’umma a cikin kangin talauci.

An Buƙaci Muttaqha Rabe Ya Canja Jam’iyya Saboda Ƙiyayya Da Tsangwama Da PDP Ke Nuna Ma Shi

Koken dai ya fito ne daga bakunan ‘ya’yan jam’iyyun PDP da APC a sa’ilin da su ke magana da manema labaru a Jalingo, babban birnin jihar.

Sun yi kira ga masu ruwa da tsaki a ja’iyyu a jihar ta Taraba da kada su amince da wannan tsari domin kuwa ba zai haifar da da mai ido ba.

A sa’ilin da su ke magana da jaridar Tribune, Jonathan Tsokwa, daga Wukari da Grace Tang, daga Sardauna da kuma Kabiru Zubairu, daga Jalingo, sun ce wannan tsari na masu shi ne, ba na talakawa ba kuma idan har aka kuskura aka cusa masu dantakara, sai ya riga rana faduwa a zabukkan 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram