Ƴan Sanda Sun Kama Ɓarayin Adai-daita Sahu A Jahar Rivers

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta cafke wasu ‘yan kungiyar ‘yan fashi da makami guda biyu da suka kware wajen yiwa direbobin babura masu kafa uku fashi wadanda basu ji basu gani.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal a ranar Lahadi.

Iringe-Koko ta bayyana wadanda ake zargin su ne Steve Green, mai shekaru 38, da kuma Adaugo Darlington, macen da take amfani da juna biyu wajen yaudarar masu buburan Adaidaita sahun domin nuna tausayi wajen neman taimako.

Wadanda ake zargin dai sun fito ne a matsayin fasinja, inda suka afkawa direbobin da wukake da adduna tare da tura su kasa yayin da suke ci gaba da tafiya.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kungiyar ta yi rashin sa’a a ranar 31 ga watan Maris, 2022, tare da Rumunduru Eneka a cikin karamar hukumar Obio/Akpor, lokacin da jami’an ‘yan sandan reshen Eneka, yayin da suke sintiri na yau da kullum, suka isa wurin da lamarin ya faru inda na karshe wanda lamarin ya shafa mutum daya aka samu Lasisi Akeem, an kwace masa babur dinsa mai kafa uku.

“Wanda abin ya shafa, wanda aka sareshi da adda, ya iya kwatanta babur dinsa da kuma wadanda ake zargin. Nan take jami’an ‘yan sandan suka kama biyu daga cikin wadanda ake zargin, sannan suka kwato babur din.

“A halin da ake ciki, an garzaya da wanda lamarin ya shafa zuwa asibiti domin kula da lafiyarsa yayin da ake kokarin cafke sauran biyun da suka tsere ana cigaba da bincike.”

A wani labarin kuma, jami’an ‘yan sandan karamar hukumar Etche da ke aiki da sahihan bayanan sirri, sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda a Okehi Etche, inda suka cafke wasu maza biyu da ake zargi.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana sunayensu da Njoku Chimanya mai shekaru 19 da kuma Chijioke Umesurum mai shekaru 20.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram