Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Ciyarwar Watan Ramadan

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa da watan Ramadan na bana da nufin rage radadin da marasa galihu ke ciki.

Da yake jawabi yayin kaddamar da shirin a harabar kamfanin buga jaridu na jihar Kano, mukaddashin gwamnan jihar, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya bukaci ‘yan kwamitin da su yi adalci wajen gudanar da ayyukansu.

Gawuna, wanda ya yi dogon bayani kan muhimmancin ciyar da mabukata a addinin Musulunci musamman a wannan wata na Ramadan, ya yi kira ga jama’a da su ba da gudummuwa domin la’akari da muhimmancinsa.

Tun da farko, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Murtala Sule Garo, ya ce gwamnati ta ware naira miliyan 550 domin samun nasarar shirin ciyar da abinci a cibiyoyi 140 dake fadin kananan hukumomi takwas na jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa kayayyakin abincin da aka bayar domin tabbatar da gudanar da shirin sun hada da buhunan shinkafa, wake, gari, gero, dabino da kuma man gyada.

Garo ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na taimakawa marasa galihu a cikin al’umma.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, Lawan Hamisu Danhassan ya fitar, ta ce shugaban karamar hukumar Kano, Alhaji Faizu Alfindiki, ya yabawa kokarin gwamnatin jihar, inda ya yi kira ga ‘yan kwamitin ciyar da jihar da su kasance masu gaskiya da adalci wajen gudanar da aikinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram