Gwamnatin Kenya Za Ta Biya Basussukan Tallafin Man Fetur Domin Daƙile Wahalar Sa

Jami’an Gwamnatin Kenya a yau Litinin din nan sun ce gwamnati za ta biya bashin tallafin mai ga dillalan man fetur a wannan makon a kokarinta na kawar da fargabar wahalar man fetur ɗin.

Kenya dai na cikin rikici ne sakamakon hauhawar farashin danyen mai tun daga shekarar 2021, wanda ya tilasta mata fara rage farashin ƴan kasuwa kamar sauran kasashen da ke kan iyakar ta.

Gwamnatin, wacce ta ke mafi girman tattalin arzikin gabashin Afirka, ta fitar da tallafin mai a watan Afrilun 2021 don rage farashin mai a kasuwannin duniya.

Ya zuwa yanzu dai ƙasar ta kashe biliyan 36, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 313) wajen tallafa wa mai, wanda hakan ya taimaka wajen daidaita farashin man fetur da kuma ci gaba da hauhawar farashin kayayyaki a cikin rukunin da gwamnati ta fi so.

Babban sakatare a ma’aikatar man fetur da ma’adinai ta ƙasar, Andrew Kamau ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa haihuwar ta baya-bayan nan ta haifar da matsalar kwararar kuɗaɗe a wasu ƙananan dillalan mai.

Kamau ya ce hakan ya haifar da karancin kayayyaki, kuma wahalhalun da ake fuskanta na da nasaba da jinkirin biyan tallafin da gwamnati ke baiwa kamfanonin.

Ya kara da cewa gwamnati na bin kamfanonin bashin biliyan 13 wanda za a daidaita a cikin makon nan.

“Wannan karanci ne,” in ji Kamau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram