Hukumar NDLEA Ta Kama Tramadol Na Kimanin Naira Biliyan 5 A Jihohi 3

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, ta kama ƙwayoyin Tramadol da Exol 5 wajen guda miliyan 9.5 da kuɗin su ya kai kimanin Naira Biliyan 5 a jihohi uku.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Wayar da kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.

Babafemi ya bayyana cewa an kama ƙwayoyin ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, MMIA, Legas, Abuja da kuma Jihar Edo.

Ya ce an gudanar da sunayen kama kayan ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Kwastan ta Ƙasa, NCS.

“Daga cikin adadin, a kwai kwali 214 na Tramadol 225 masu ɗauke da sunaye daban-daban har guda 10, wadanda su ka zama adadin 9, 219, 400 masu nauyin kilogiram 6, 384.5, wadanda kudinsu ya kai N4, 609, 700, 000 a ranar Talata 29 ga Maris. .

“Wannan ya zo ne bayan kama kwali 85 na busasshen ganyen Khat mai nauyin kilo 1,327.35 da hukumar kwastan ta MMIA ta NDLEA ta yi a matsayin alamar hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro biyu.

“A Abuja, an kama kimanin ƙwayoyi 228,740 da kafso-kafso na Tramadol da Exol 5 a ranar Juma’a, 1 ga Afrilu, a unguwar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja. An loda kayan ne a mota a Legas inda ta nufi Kano.

“Ko da yake direban motar ya tsere cikin daji a lokacin da ake binciken motar, wasu mataimakansa biyu; Usman Abdulmumini mai shekaru 23 da Aminu Ahmad mai shekaru 22 an kama su,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram