Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP kuma ɗan takarar gwamna a jahar Katsina, Salisu Yusuf Majigiri ya ce idan ya zama gwamnan jahar zai zo da tsare-tsaren da za su magance matsalar tsaro.
Salisu Majigiri ya bayyana haka ne a yayin wata fira da ya yi da wakilin gidan talabijin na Arise a Katsina a warin gangamin nuna aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
A cikin bayaninsa, Majigiri ya ce idan har ya samu mulkin jahar, cikin kwanaki 100 zai mayar da duk ƴan gudun hijira muhallansu, ya kuma sama ma manoma damar ci gaba da aikin guna tare da buɗe duk makarantun da aka rufe saboda ƴan ta’adda.