Mafarauta 4 Sun Mutu, 7 Sun Jikkata Bayan Fashewar Wani Bam A Hanyar Borno

Wasu mafarauta sun bayyana cewa, akalla mutane hudu ne suka mutu, bakwai Kuma suka jikkata, yayin da suka ta ka Wani abun fashewar da akae kyautata zaton yan tada kayar baya ne suka birne a kan Babban hanyar Borno

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya afku ne da musalin karfe 10:00 na safen ranar Asabar tsakanin garin Damboa da Sabon gari, na karamar hukumar Damboa dake jihar ta Borno.

Kana an ruwaito cewa, Motar mafarautar ta yi matukar lalacewa, yayin da wasu daga cikin ke cikin wani mawuyacin Hali.

Guda daga cikin mafarautan mai suna Bura Mohammed ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa, sun fita sintiri ne, lokacin da suka taka abun fashewar.

Kazalika ya bayyana cewa tuni akayi Jana’izar wadanda suka mutu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda Kuma wadanda suka jikkata ke kwance a Babban Asibitin gwamnatin Tarayya dake Biu.

Sai dai harkawo hada wannan rahoton rundunar sojin kasar nan bata ce komai ba dangane da wannan lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram