Matsalar Tsaro: Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Yi Fatali Da Ƙudirin El-Rufa’i Na Gayyato Sojojin Haya

Ƙungiyar Dattawan Arewa wato ACF ta yi fatali da Kudirin Gwamnan Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna kan kawo Sojojin haya idan gwamnatin Tarayya ta gaza shawo kan matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta.

El’rufai yayi wannan iƙirarin ne tun bayan ta’azzarar hare-haren Yan bindiga a jihar Kaduna, ciki har da na ranar Litinin din data gabata inda farmaki Yan bindiga kan jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya hallaka Mutum 9 tare da awon gaba da akalla mutum 21.

Kazalika a cikin wata sanarwa da Sakataren Kungiyar Murtala Aliyu ya fitar a jiya Lahadi, ya ce shawo kan matsalar tsaro ya rataya ne a wuyan gwamnatin Tarayya don haka akwai bukatar a kwantar da hankula wajan lalubu hanyoyin da za’a warware matsalar.

A cewar sanarwar, gayyatar sojojin kasashen waje ko sojojin hayar, “dole ne a yi taka-tsan-tsan kan irin wannan mataki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram