Fadar shugaban Najeriya ta yi ikirarin cewa ‘yan siyasar PDP sun kwashe dala biliyan 20 a shekarar karshe ta mulki su.
Fadar shugaban kasar na maida martani ne ga wata takardar sanarwar karshen taron PDP, wadda a cikin ta jam’iyyar ta soki gwamnatin APC, tana bayyana ta da cewar ta gaza hassala komai.
A cikin wata sanarwar fadar gwamnatin da mai magana da yawun ta, Garba Shehu ya raba wa manema labaru ranar Lahadi, ya ce, PDPn kawai na kokarin rufe jerin munanan laifukkan da suka tafka ne a tsawon lokacin da suka dauka bisa mulki.
Ya ce, wadancan dimbin munanan laifukka su ne gwamnatin Buhari da jam’iyyar PDP suka yi ta yin kokarin gyarawa a cikin shekaru 7 da suka kwashe suna jagorancin kasar.
A cewar sanarwar, gwamnati mai ci ba za ta taba mantawa da yadda almundahanar gwamnatin PDP ta sanya albashin sojoji ya rinka tafiya aljifan ‘yan siyasa ba a yayin da sojojin suka rinka mutuwa a bakin daga, sannan kasashen turai suka ki sayar wa Najeriya makamai a dalilin rashin gaskiyar waccan gwamnatin.
A yau ga jam’iyyar APC da sojojin da ke tunkaho da isasun kayan aiki, ga jiragen yaki daga kasashen da a da suka ki bai wa gwamnatin PDP, ana samun nasarar kawar da Boko Haram, sannan an hallaka jagoran kungiyar ISWAP a cikin luguden da aka yi ta sama a Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa da gangan kuma ‘yan siyasar PDP suka rura wutar rikicin kabilanci da na addini, inda suka ma ki samar da masalaha dangane da rikicin makiyaya da manoma wanda ya zama ruwan dare a zamanin mulkin su mai cike da kura-kurai.