Tsohon shugaban jam’iyyar APC kuma sakataren jam’iyyar yanzu a jahar Katsina, Malam Shitu S Shitu ya bayyana cewa Jam’iyyar na dada samun karuwar mutane masu shigowa cikinta.
Sakataren ya bayyana haka ne a ofishin jam’iyyar na jaha a lokacin da daya daga cikin yan takarar gwamnan Katsina, Abdulkarim Dauda ya ziyarce su domin nuna aniyarsa ta son zama gwamnan jahar.
Kalli cikakken labarin a cikin wannan hoton bidiyon da ke kasa.
Shitu ya ce jagoranci na gari da jam’iyyar ta su ta APC ta samu ya sanya ake mata tururuwa ana shigowa a ciki.
Tun da farko dan takarar gwamnan Abdulkarim Dauda ya gode ma jam’iyyar bisa ga damar da ta bashi don ya zo ya nuna sha’awarsa ta shiga jerin yan takarar da suka fito a jahar ta Katsina.
Dauda ya samu rakiyar matasa mata da maza magoya bayansa.