ALH ABDULKARIM DAUDA YA BAYYANA KUDIRIN TAKARAR GWAMNAN JAHAR KATSINA

A ranar lahadi 3 ga watan Afrilu 2022 ne shahararren dansiyasa kuma tsoho jami’in Dansanda Alhaji Abdulkarim Dauda ya bayyana kudirin sa na tsayawa takarar gwamnan jahar Katsina a babban zaben 2023 da za’a gabatar badi.

Dantakarar ya shiga babban ofishin jama’iyar APC na jahar Katsina tare da magoya bayansa, inda yaje ya fara da gaishe da shuwagabannin jama’iya wanda daga bisani ya gabatar da kudirinsa na tsayawa takarar Gwamnan Jahar Katsina a zaben 2023.

Shugaban jama’iyar na Jahar Sani Ali Ahmed ya bayyana matukar farin cikin zuwan Dantakarar Alh Abdulkarim Dauda, inda yace “Jama’iyar APC nayi maku maraba dakai da jama’ar ka, kuma ka same mu mutane masu adalci ga dukkan ‘yan takarkari, munji dadi yadda ka kalli mutunci jama’iyar mu, kuma muna yi maka maraba da  fatan alkhairi, zamu baka dama ka gabatar kudirinka ga jama’iya

Abdulkarim ya fara jawabin sa da godiya yana mai cewa “Ina mai godiya da kuka bani dama, sannan ina mai sanar da Jama’iya kudirina na tsayawa takarar Gwamnan Jahar Katsina a zaben 2023, a karkashin wannan jama’iya tamu mai albarka, wadda damu aka kafa wannan jama’iyar, shiyasa na kawo kaina don na gabatar da kaina a gareku shuwagabannin Jama’iyar APC na Jahata Jahar Katsina“.

Bayan kammala bayanan sa ne, ya mikawa shugaban jama’iyar takardar kudirin nasa na tsayawa takarar Gwamnan Jahar Katsina a zabe mai zuwa.

Tarihi dai ya nuna babu wanda ya taba neman tsayawa takarar gwamnan Jahar Katsina daga yankin da Alh Abdulkarim Dauda ya fito watau (DAURA) shine mutum na farko da ya fito ya kuma bayyana kudirinsa, yankin KATSINA dana FUNTUA sunyi Gwamna wannan yasa wasu suke ganin wannan dalilin zai iya sanya shi cin nasarar wannan zaben.

Idan za’a tuna a baya wannan Dantakara yasha kiraye kiraye daga jama’ar wannan Jaha kan ya fito ya nemi takarar Gwamnan jahar Katsina, wanda yanzu a karshe ya amsa masu kiraye kirayen da suke yi masa na tsayawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram