Dole ayi gaggawar kawo Ƙarshen Kisan da Ƴan ta’adda suke yiwa Ƴan Najeriya — Tinubu ga Buhari

Dole ayi gaggawar kawo Ƙarshen Kisan da Ƴan ta’adda suke yiwa Ƴan Najeriya — Tinubu ga Buhari

Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa, Bola Tinubu ya gayawa Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da a tabbatar an tsaida Kisan da Ƴan Ta’adda suke yiwa Ƴan Najeriya.

Tinubu ya bayyana cewar hare-haren da suka haɗa da saka ban a Jirgin Ƙasa na Abuja-Kaduna a tsakanin Katari da Rigina, inda kuma ƴan Ta’adda suka buɗe wuta a ƴan Ƙasa Matafiya, baza’a taɓa yarda dashi ba.

Tsohon Gwamnan Jahar Lagos ya bayyana haka, bayan ya ziyarci Gwamnan Jahar Kaduna Nasir El-Rufa’i a ranar Talata, akan harin da ƴan bindiga suka kai.

Tinubu, wanda ya ziyarci El-Rufa’i, ya bada kyautar Naira Miliyan 50 ga waɗanda lamarin ta’addancin Jirgin ya shafa, sun kuma ziyarci Asibitin da aka kai wanda iftila’in ya shafa.

“Harin da kisan wanda ƴan ta’adda suka yi a kowane irin manufa bazamu taɓa yarda dashi,” inji Tinubu.

“Ina kira ga Gwamnatocin Tarayya da Jaha dasu yi aiki tuƙuru domin magance wannan matsalar ta’addanci,” Inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram