2023: Jam’iyyar APC Tace Fom Ɗin Tsayawa Takara Ga Mata Kyauta Ne

Shugaban Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar APC, Sanata Abdulahi Adamu, ya kaddamar da fom din tsayawa takara kyauta ga mata masu neman tsayawa takara a zaben 2023.

Jam’iyyar mai mulki ta ce hakan na daga cikin kokarin ganin an shigar da mata cikin harkokin siyasa da kuma kawo karshen wariyar da akewa mata .

Shugabar mata ta jam’iyyar ta kasa, Ms Betty Edu ta bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a sakatariyar jam’iyyar ta kasa dake Abuja.

A kalamanta ta bayyana cewa: “Mu ne jam’iyya mafi girma a Afirka kuma muna so mu yi wata kwakkwarar sanarwa cewa mun tsaya kan hada kai, wajen ba da fifiko ga mata. Jam’iyyar ta riga ta amince da cewa mata zasu tsaya takara da fom din tsayawa takara kyauta.

“Sun jefa kwallon a filinmu. Kafin yanzu muna da mata suna cewa ba zamu iya biyan fam ɗin takara ba. An ba mu dama mafi girma da za mu iya fitowa a matsayin wanda zasu lashe zabe domin za mu yi takara ne a kan tikitin jam’iyya mai mulki.

Ta kara da cewa ba wai jam’iyya mai mulki kadai ba, jam’iyyar da ta taka rawar gani, jam’iyyar da ta samar da walwala ga Nijeriya, jam’iyyar da ta shirya tsaf domin ganin mata a cikinta.”

Shugabar matan ta ce jam’iyya mai mulki na baiwa matan abin da ya haura kashi 35 cikin 100 na tabbatar da hakan.

Edu ta bukace su dasu shiga cikin jerin tsare-tsare da za su kai ga cin nasara a zaben 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram