Shelkwatar tsaro ta ƙasa, ta ce wani fitaccen kwamanda a ƙungiyar ƴan ta’adda ta Boko Haram, Saleh Mustapha, ya mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai, a yankin Arewa-maso-Gabas, inda ya zuwa yanzu ƴan ta’adda 51,114 ne su ka miƙa wuya.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka a yau Alhamis a Abuja, yayin da ya ke zantawa da manema labarai kan ayyukan da sojoji su ka yi tsakanin ranar 25 ga Maris zuwa 7 ga Afrilu.
Onyeuko ya ce mika wuyan Mustapha, wanda a ka fi sani da Ibn Kathir, wanda shi ne Qaid na Garin Ba-Abba ga sojoji a Bama ya na da matukar muhimmanci.
Ya kara da cewa adadin ƴan ta’adda 51,114 da iyalansu da su ka hada da maza 11,398, mata 15,381, yara 24,335 sun mika wuya ga sojoji ya zuwa 5 ga Afrilu.
A cewarsa, an tattara bayanan duk ƴan ta’addan da su ka miƙa wuya, yayin da waɗanda a ka kama, da fararen hula da a ka ceto da kuma kayayyakin da aka kwato an mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki.
Ya ce a cikin makonni biyun da suka gabata sojojin sun kwato tankar yaki guda daya, bindigu, manyan bindigogi biyar, bindigogin GTS guda biyu da kuma bindigogin AA guda uku da sauran kayayyakin yaƙi a gurin ƴan ta’addan.