Ƴan bindiga sun kashe ƴan gudun hijira guda 2 a Ƙaramar Hukumar Barki Ladi ta Jahar Filato.
An gano cewa wanda lamarin ya shafa, wanda suka yi gudun hijira daga yankunan su a ƙauyen Ratis na Ƙaramar Hukumar, sun dawo ga yankunan su, sun sake gina gidajen da aka lalata, a lokacin da ƴan bindiga suka kai hari.
Shugaban Ƙungiyar Matasan Berom Dalyop Mwantiri ya tabbatar da kisan ga Jaridar PUNCH a Jos a ranar Alhamis.
A cewar sa, sun kuma jikkata wasu mutane 3 a lokacin kai harin.
Shugaban Matasan yace, “an sake samun wani mummunan lamari a ƙauyen Rantis, gundumar Gashish ta Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jahar Filato, inda suka kai hari ga Ƴan Gudun Hijira da misalin ƙarfe 3:30 na ranar 6 ga watan Afrilu na shekarar 2022. A dalilin haka, an tabbatar mutane sun mutu, 3 sun jikkata.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Ubah Ogaba ba’a same shi a waya ba a lokacin da aka kira shi domin jin tabbaci.