Hukumar Hisbah a Jigawa ta ƙwace Kwalabanin Giya 1,426 a Ƙananan Hukumomi guda biyu na Jahar.
Kwamandan Hisbah na Jaha Ibrahim Ɗahiru, ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Dutse, Babban Birnin Jahar a ranar Alhamis.
Ɗahiru ya bayyana cewar sun kuma ƙwace Jarka mai lita 25 na giyar Hausa Burkutu.
Ya bayyana cewar an ƙwace giyar a lokacin da Jami’an Hisbah suka kai samame a Otal, da Mashaya a Ƙananan Hukumomi guda biyu.
Kwamandan ya ƙara dacewa, mutane 15 da ake zargi da suka haɗa da mata, an kama su a lokacin kai farmakin.
A cewar sa, Kwalabanin Giya 177, da Jarka 25 na Burkutu, da mutane 14 a ranar 3 ga watan Afrilu, a Ƙaramar Hukumar Gumel.
Yace, ” Hisbah ta kama mutane 3 a Ƙaramar Hukumar Gumel a wani Otal na Awala, Dake kan hanyar Gujungu, da Sabuwar Sahara a bayan Sakatariyar Ƙaramar Hukumar da Gidan Mama mai Burkutu.
“A wannan kai harin, mun kama mutane 14, da suka haɗa da wadda ke saida Burkutu.