Saudiyya Zata Tallafawa Yemen Da Dala Miliyan 3

A yau Alhamis ne Saudi Arebiya ta sanar da bayar da tallafin dala biliyan uku ga kasar Yemen, bayan kafa kwamitin Shugabancin Yemen ɗin.

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, tallafin ya hada da dala biliyan biyu na haɗin gwiwa tsakanin masarautar da Hadaddiyar Daular Larabawa, inda su ka bai wa babban bankin kasar Yemen.

Haka kuma ta ce ta haɗa da dala biliyan ɗaya da ga ƙasar Saudiyya, inda dala miliyan 600 za ta ba da kudaden sayan kayayyakin man fetur da kuma dala miliyan 400 don tallafa wa ayyukan raya kasa da tsare-tsare.

Saudi Arabiya ta kuma sanar da bayar da dala miliyan 300 ga shirin ba da agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, MDD a shekarar 2022 don rage radadin al’ummar Yemen.

A halin da ake ciki, Masarautar ta buƙaci sabuwar majalisar Yemen da aka kafa da ta fara tattaunawa da ƴan Houthis, karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya domin cimma matsaya ta karshe domin samar da maslaha ta siyasa.

Tun da farko Shugaban Ƙasar Yemen Abd-Rabbu Mansour Hadi, ya sanar da kafa kwamitin shugabancin kasar, tare da mika ragamar mulki ga majalisar domin ci gaba da gudanar da ayyuka a lokacin rikon kwarya.

Kasar Yemen dai ta fada cikin yakin basasa tun shekara ta 2014 lokacin da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran su ka kwace iko da wasu lardunan arewacin kasar tare da tilastawa gwamnatin Yemen Hadi mai samun goyon bayan Saudiyya ficewa daga babban birnin kasar Sanaa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram