Rundunar ƴan sanda a Jihar Kogi ta ceto fasinjoji 12 da ga hannun wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Edward Egbuka ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, a wata sanarwa da kakakin rundunar jihar, SP William Ovye-Aya ya fitar.
Egbuka ya ce mutanen 12 da abin ya rutsa da su sun fito ne daga wata motar fasinja mai cin mutane 16 da ke kan hanyar Benue, inda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka tsare motar kan hanyar Anyigba zuwa Ankpa.
CP ya ce: “Rundunar ‘yan sandan ta samu wani rahoto da ke nuna cewa wata motar bas Toyota mai lamba 192 XA, da wani Benard Ejeh ke tuka fasinjoji 16 daga Abuja zuwa Jihar Binuwai ta hanyar ANKPA, ta ci karo da masu garkuwa da mutane a kauyen Ojuwo-Ajebgo na Karamar Hukumar Ofu, kan titin Anyigba.
“Ba tare da bata lokaci ba, jami’an hukumar Quick Response Unit dake Itobe, nan take suka fara kai farmaki, suka bi sahun barayin cikin daji suka ceto fasinjoji 12 ciki har da direban yayin da ba a ga sauran fasinjoji 4 ba.
“An yi sa’a kuma, na kai ziyarar gani da ido zuwa yankin mazaɓar sanata ta Kogi ta Gabas, don haka lokacin da na samu labarin yayin da nake kan hanyar zuwa Ejule, nan da nan na wuce wurin, inda na gana da fasinjojin da aka ceto,” in ji CP.
Egbuka, ya yi tir da rahoton karya da aka yi a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa sama da Fasinjoji 15 ne suka bace sakamakon lamarin.