Dingyaɗi Ya Bayyana Dalilan Da Suka Sanya Baza’a Bar Ƴan Najeriya Su Mallaki Makami Ba

Ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Dingyadi, ya ce rashin tsaro a kasar zai kara ta’azzara idan aka bar ‘yan Najeriya su rike makamai.

Ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Alhamis a wani taron manema labarai a Abuja, yayin da yake amsa tambaya kan kiran da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Ado Doguwa ya yi.

A makon da ya gabata Doguwa ya ce ” Ya Kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu duba da yadda yana yin halin tsaro ya tabarbare a ciki a kasar.”

Dingyadi ya ce, “Muna yin duk abin da za mu iya don ganin mun rage yaduwar bindigogi a tsakanin yawancin ‘yan Najeriya.

“Ya kamata mu takaita wannan ga mutanen da ya kamata su mallake su, wadanda ya kamata su yi amfani da su, wadanda aka koya musu amfani da su da kuma wadanda ke da damar yin amfani da su.”

“In ba haka ba, idan kun sanya shi duka al’amuran mutane, zai kara dagula lamarin. Wannan shine ra’ayina na gaskiya kan wannan batu.

Dingyadi yace “ba ni da wannan ra’ayi a halin yanzu, ba na goyon bayan hakan,” in ji Ministan.

Ya kara da cewa ma’aikatar sa na yin duk mai yiwuwa domin ganin an fara aiwatar da aikin karin albashi ga jami’an ‘yan sanda a fadin kasar nan da cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram