Shugaban hukumar kanana da matsakaitan sana’o’i na Najeriya kuma ciyaman na gidauniyar Gwagware, Dikko Umar Radda ya bayyana yadda al’ummar jahar Katsina suka nemi ya fito takarar gwamnan jahar.
Dikko Radda ya furta haka ne a yayin da ya kai ziyara a ofishin jam’iyyar APC na jahar Katsina a ranar Assabar din nan.
Ya ce abinda ya sa ya fito saboda ya amsa kiran mutane daga mazabu 361 da ke fadin jahar wadanda ya ce sun je sun same shi har gida suka mika kokon bararsu ta ya zo ya tsaya takarar gwamna.
Radda ya yi amfani da wannan damar ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun tsaida ma jahar Katsina mutumin kirki.