Tsahon gwamnan jahar Katsina Ibrahim Shema, ya roƙi mutanen Katsina Katsina da su taimaka su bai wa jam’iyyar PDP ƙuru’unsu a zaɓen ƙananan hukumomin jahar da za a gudanar a ranar Litinin 11 ga watan 4 na shekarar 2022.
Shema ya yi wannan maganar ne a cikin wata muryarsa da ya yi kuma muka same ta a shafin Facebook na wani matashi da ke tare dasu mai suna Yusuf Mai Iyali.
Bayan roƙo da tsohon gwamnan ya yi ya kuma buƙaci da alummar su nuna nadamarsu ta zaɓen APC da suka yi a baya, su zaɓi PDP a yanzu.