Shugaban hukumar ƙanana da matsakaitan sana’o’i na Najeria kuma mai son tsayawa takarar gwamnan jahar Katsina karkashin tutar jam’iyyar APC, Dr Dikko Umar Radda ya bayyana ce wa shi ba zai yi sasanci ba da ƴan ta’adda idan ya zama gwamna.
Dikko Radda ya faɗi haka ne a yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labara jim kaɗan bayan bayyana ƙudurorinsa da zai aiwatar idan ya samu mulkin jahar a ofishin sa na yaƙin neman zaɓe da ke Katsina.
Radda ya ce, ba maganar sasanci da ƴan ta’adda sai dai in su da kansu suka ji wuta suka nemi ayi ma su afuwa to sannan ne za a duba yiwuwar abinda za a yi ma su domin su koma mutanen kirki.
Daga cikin abubuwan da ya ke so gwamnatinsa ta aiwatar, akwai bunƙasa harkar noma da kiwon lafiya da tsaro da tattalin arziƙi tare da ilimi.
Ya ƙara da cewa zai yi ƙoƙarin shigo da tsarin koya turanci da lissafi a makarantun allo saboda ya ce duk mutumin da ya iya sanin al’qur’ani to babu abinda zai mashi wuya aduniya.